Gwamnatin Kano za ta dauki lauyoyi 70 aiki

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da daukar lauyoyi 70 aiki a wani yunkuri na gwamnatinsa don bunkasa damar samun aiki da kuma karfafa bangaren shari’a na jihar.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama’a a ofishin shugaban ma’aikatan gwamnati na jihar Kano, Aliyu Yusuf ya fitar a safiyar Juma’a.

A yayin kula da tantancewar karshe ga wadanda aka zaba, shugaban ma’aikatan gwamnati, Abdullahi Musa, ya yabawa gwamnati bisa hangen nesa da ta yi, yana jaddada cewa bangaren shari’a ya dade yana jiran irin wannan cigaban.

Ya kuma karfafa guiwar sabbin lauyoyin da aka dauka su nuna halaye nagari, jajircewa, aiki tukuru, da kuma kasancewa masu tsoron Allah wajen aiwatar da ayyukansu.

Haka zalika, Musa ya gargadi wadanda aka dauka da su kasance jakadu nagari ga jihar Kano.

Ya bayyana kwarin guiwa cewa wannan mataki zai taimaka kwarai wajen inganta ayyukan shari’a a jihar.

Leave a Comment