Yan sanda sun kama ma’aikacin bankin da ya sace N18m daga abokin hulda

Rundunar yan sandan jihar Katsina ta kama wani jami’in banki a Daura bisa zargin sace N18m daga asusun wani abokin huldar bankin ta hanyar na’urar ATM.

Wanda ake zargin, shi ne mataimakin jami’in ayyuka a wani banki, an zarge shi da hada baki da abokansa domin aikata laifin.

ASP Abubakar Aliyu, kakakin rundunar yan sandan Katsina, ya tabbatar da kamen yayin wani taron manema labarai a hedikwatar yan sandan jihar Katsina ranar Alhamis.

ASP Aliyu ya bayyana cewa an fara bincike kan batun ne bayan da wanda abin ya shafa, Okojie Herbert, ya kai rahoton abin da ya faru.

“Bayan samun korafi daga Okojie Hubert Erayomon, mazaunin Daura, wanda ke matsayin mataimakin shugaban ayyuka a Access Bank, reshen Daura, kan zargin almundahanar da aka yi wa Adewumi Bolaji Gabriel, mai shekara 28, shugaban ATM na bankin Access reshen Daura, Jihar Katsina, an gano cewa wanda ake zargin ya haɗa baki da abokinsa, David Mesioye, ma’aikacin Access Bank reshen Kafur, wanda yanzu haka ya tsere, domin sace naira miliyan goma sha takwas da dubu dari ɗaya da sittin da huɗu (₦18,164,000.00) daga asusun wani abokin huldar banki.”

Ya kara da cewa jami’an tsaro suna nan suna neman abokin wanda ake zargin da ya tsere don gurfanar da shi gaban kuliya.

Leave a Comment